# ha/gumi.xml.gz
# it/piccardo.xml.gz
(src)="s1.1"> Da sũnan Allah , Mai rahama , Mai jin ƙai .
(trg)="s1.1"> In nome di Allah , il Compassionevole , il Misericordioso
(src)="s1.2"> Godiya ta tabbata ga Allah , Ubangijin halittu ;
(trg)="s1.2"> La lode [ appartiene ] ad Allah , Signore dei mondi
(src)="s1.3"> Mai rahama , Mai jin ƙai ;
(trg)="s1.3"> il Compassionevole , il Misericordioso ,
(src)="s1.4"> Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako .
(trg)="s1.4"> Re del Giorno del Giudizio .
(src)="s1.5"> Kai muke bauta wa , kuma Kai muke neman taimakonKa .
(trg)="s1.5"> Te noi adoriamo e a Te chiediamo aiuto .
(src)="s1.6"> Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya .
(trg)="s1.6"> Guidaci sulla retta via ,
(src)="s1.7"> Hanyar waɗanda Ka yi wa ni 'ima , ba waɗanda aka yi wa fushi ba , kuma ba ɓatattu ba .
(trg)="s1.7"> la via di coloro che hai colmato di grazia , non di coloro che [ sono incorsi ] nella [ Tua ] ira , né degli sviati .
(src)="s2.1.0"> A. L ̃ .
(src)="s2.1.1"> M ̃ .
(trg)="s2.1"> Alif , Lâm , Mîm .
(src)="s2.2"> Wãncan ne Littãfi , bãbu shakka a cikinsa , shiriya ne ga mãsu taƙawa .
(trg)="s2.2"> Questo è il Libro su cui non ci sono dubbi , una guida per i timorati ,
(src)="s2.3"> Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi , kuma suna tsayar da salla , kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa .
(trg)="s2.3"> coloro che credono nell' invisibile , assolvono all' orazione e donano di ciò di cui Noi li abbiamo provvisti ,
(src)="s2.4"> Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka , da abin da aka saukar daga gabãninka , kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni .
(trg)="s2.4"> coloro che credono in ciò che è stato fatto scendere su di te e in ciò che è stato fatto scendere prima di te e che credono fermamente all' altra vita .
(src)="s2.5"> Waɗannan suna kan shiriya , daga Ubangjinsu , kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara .
(trg)="s2.5"> Quelli seguono la guida del loro Signore ; quelli sono coloro che prospereranno .
(src)="s2.6"> Lalle ne waɗanda suka kãfirta daidai ne a kansu , shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba , ba zã su yi ĩmãni ba .
(trg)="s2.6"> In verità [ per ] quelli che non credono , non fa differenza che tu li avverta oppure no : non crederanno .
(src)="s2.7"> Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu , da a kan jinsu , kuma a Kan ganin su akwai wata yãna ; kuma suna da wata azãba mai girma .
(trg)="s2.7"> Allah ha posto un sigillo sui loro cuori e sulle loro orecchie e sui loro occhi c'è un velo ; avranno un castigo immenso .
(src)="s2.8.0"> Kuma akwai daga mutãne wanda yake cewa : " Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira . "
(src)="s2.8.1"> Alhãli kuwa su ba muminai ba ne .
(trg)="s2.8"> Tra gli uomini vi è chi dice : “ Crediamo in Allah e nel Giorno Ultimo !” e invece non sono credenti .
(src)="s2.9"> Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni , alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu , kuma bã su sakankancẽwa !
(trg)="s2.9"> Cercano di ingannare Allah e coloro che credono , ma non ingannano che loro stessi e non se ne accorgono .
(src)="s2.10.0"> A cikin zukãtansu akwai wata cũta .
(src)="s2.10.1"> Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta , kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya .
(trg)="s2.10.0"> Nei loro cuori c'è una malattia e Allah ha aggravato questa malattia .
(trg)="s2.10.1"> Avranno un castigo doloroso per la loro menzogna .
(src)="s2.11"> Kuma idan aka ce musu : " Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa , " sukan ce : " Mũ mãsu kyautatawa kawai ne ! "
(trg)="s2.11"> E quando si dice loro : “ Non spargete la corruzione sulla terra” , dicono : “ Anzi , noi siamo dei conciliatori !” .
(src)="s2.12"> To , lalle ne su , sũne mãsu ɓarna , kuma amma bã su sansancewa .
(trg)="s2.12.0"> Non sono forse questi i corruttori ?
(trg)="s2.12.1"> Ma non se ne avvedono .
(src)="s2.13.0"> Kuma idan aka ce musu : " ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni , " sukan ce : " Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni ? "
(trg)="s2.13.0"> E quando si dice loro : “ Credete come hanno creduto gli altri uomini” , rispondono : “ Dovremmo credere come hanno creduto gli stolti ?” .
(src)="s2.13.1"> To , lalle ne su , sũ ne wãwãye , kuma amma bã su sani .
(trg)="s2.13.1"> Non sono forse loro gli stolti ?
(trg)="s2.13.2"> Ma non lo sanno .
(src)="s2.14.0"> Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni , sukan ce : " Mun yi ĩmãni .
(src)="s2.14.1"> " Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu , sukan ce : " Lalle ne muna tãre da ku : Mu mãsu izgili , kawai ne . "
(trg)="s2.14"> Quando incontrano i credenti , dicono : “ Crediamo” ; ma quando sono soli con i loro dèmoni , dicono : “ Invero siamo dei vostri ; non facciamo che burlarci di loro” .
(src)="s2.15"> Allah Yana yin izgili gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu , suna ɗimuwa .
(trg)="s2.15"> Allah si burla di loro , lascia che sprofondino nella ribellione , accecati .
(src)="s2.16"> Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya , sai fataucinsu bai yi rĩba ba , kuma ba su kasance masu shiryuwa ba .
(trg)="s2.16.0"> Sono quelli che hanno scambiato la retta Guida con la perdizione .
(trg)="s2.16.1"> Il loro è un commercio senza utile e non sono ben guidati .
(src)="s2.17"> Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta , to , a lõkacin da ta haskake abin da yake gẽfensa ( na abin tsõro ) , Allah Ya tafi da haskensu , kuma Ya bar su a cikin duffai , bã su gani .
(trg)="s2.17"> Assomigliano a chi accende un fuoco ; poi , quando il fuoco ha illuminato i suoi dintorni , Allah sottrae loro la luce e li abbandona nelle tenebre in cui non vedono nulla .
(src)="s2.18"> Kurãme , bẽbãye , makãfi , sabõda haka bã su kõmõwa .
(trg)="s2.18"> Sordi , muti , ciechi , non possono ritornare .
(src)="s2.19.0"> Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama , a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya : suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin , dõmin tsõron mutuwa .
(trg)="s2.19.0"> [ O come ] una nuvola di pioggia nel cielo , gonfia di tenebre , di tuoni e di fulmini : mettono le loro dita nelle orecchie temendo la morte a causa dei fulmini .
(src)="s2.19.1"> Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai !
(trg)="s2.19.1"> E Allah accerchia i miscredenti .
(src)="s2.20.0"> Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu , ko da yaushe ta haskakã musu , sai su yi tafiya a cikinta , kuma idan ta yi duhu a kansu , sai su yi tsaye .
(trg)="s2.20.0"> Il lampo quasi li acceca : ogni volta che rischiara , procedono ; ma quando rimangono nell' oscurità si fermano .
(src)="s2.20.1"> Kuma dã Allah Yã so , sai Ya tafi da jinsu da gannansu .
(trg)="s2.20.1"> Se Allah avesse voluto , li avrebbe privati dell' udito e della vista .
(src)="s2.20.2"> Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne .
(trg)="s2.20.2"> In verità Allah su tutte le cose è potente .
(src)="s2.21.0"> Yã ku mutãne !
(src)="s2.21.1"> Ku bauta wa Ubangjinku , Wanda Ya halicce ku , kũ da waɗanda suke daga gabãninku , tsammãninku ku kãre kanku !
(trg)="s2.21"> O uomini , adorate il vostro Signore Che ha creato voi e quelli che vi hanno preceduto , cosicché possiate essere timorati .
(src)="s2.22.0"> Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa , kuma sama gini , kuma Ya saukar da ruwa daga sama , sa 'an nan Ya fitar da abinci daga ' ya 'yan itãce game da shi , sabõda ku .
(trg)="s2.22.0"> [ Egli è ] Colui Che della terra ha fatto un letto e del cielo un edificio , e che dal cielo fa scendere l' acqua con la quale produce i frutti che sono il vostro cibo .
(src)="s2.22.1"> Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi , alhãli kuwa kuna sane .
(trg)="s2.22.1"> Non attribuite consimili ad Allah ora che sapete .
(src)="s2.23.0"> Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bãwanmu , to , ku zõ da sũra guda daga misalinsa ( Alƙur 'ãni ) .
(src)="s2.23.1"> Kuma ku kirãwo shaidunku baicin Allah , idan kun kasance mãsu gaskiya .
(trg)="s2.23"> E se avete qualche dubbio in merito a quello che abbiamo fatto scendere sul Nostro Servo , portate allora una sura simile a questa e chiamate altri testimoni all' infuori di Allah , se siete veritieri .
(src)="s2.24"> To , idan ba ku aikata ( kãwo sura ) ba , to , bã zã ku aikataba , sabõda haka , ku ji tsoron wuta , wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne , an yi tattalinta dõmin kãfurai .
(trg)="s2.24"> Se non lo fate - e non lo farete - temete il Fuoco , il cui combustibile sono gli uomini e le pietre , che è stato preparato per i miscredenti .
(src)="s2.25.0"> Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai , cẽwa lallene , suna da gidãjen Aljanna , ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu .
(trg)="s2.25.0"> E annuncia a coloro che credono e compiono il bene , che avranno i Giardini in cui scorrono i ruscelli .
(src)="s2.25.1"> Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu ' ya 'yan itãce daga gare su , sai su ce : " Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka , " Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna , Kuma sunã da , a cikin su , mãtan aure mãsu tsarki , kuma su , cikin su madawwama ne .
(trg)="s2.25.1"> Ogni volta che sarà loro dato un frutto diranno : “ Già ci era stato concesso !” .
(trg)="s2.25.2"> Ma è qualcosa di simile che verrà loro dato ; avranno spose purissime e colà rimarranno in eterno .
(src)="s2.26.0"> Lalle ne , Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli , kõwane iri ne , sauro da abin da yake bisa gare shi .
(trg)="s2.26.0"> In verità , Allah non esita a prendere ad esempio un moscerino o qualsiasi altra cosa superiore .
(src)="s2.26.1"> To , amma waɗanda suka yi ĩmãni , sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su , kuma amma waɗanda suka kãfirta , sai su ce : " Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan ya zama misãli ? " na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi , kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi , kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai .
(trg)="s2.26.1"> Coloro che credono sanno che si tratta della verità che proviene dal loro Signore ; i miscredenti invece dicono : “ Cosa vuol dire Allah con un simile esempio ?” .
(trg)="s2.26.2"> [ Con esso ] ne allontana molti , e molti ne guida .
(src)="s2.27"> Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi , kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sãdar , kuma suna ɓarna a cikin ƙasa , waɗannan sũ ne mãsu hasãra .
(trg)="s2.27.0"> coloro che rompono il patto di Allah dopo averlo accettato , spezzano ciò che Allah ha ordinato di unire e spargono la corruzione sulla terra .
(trg)="s2.27.1"> Quelli sono i perdenti .
(src)="s2.28"> Yaya kuke kãfirta da Allah , alhãli kuwa kun kasance matattu sa 'an nan Ya rãyar da ku , sa 'nnan kuma Ya matar da ku , sa 'an nan kuma Ya rãya ku , sa 'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku ?
(trg)="s2.28.0"> Come potete essere ingrati nei confronti di Allah , quando eravate morti ed Egli vi ha dato la vita ?
(trg)="s2.28.1"> Poi vi farà morire e vi riporterà alla vita e poi a Lui sarete ricondotti .
(src)="s2.29.0"> Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya , sa 'an nan kuma Ya daidaita zuwa sama , sa 'an nan Y a aikata su sammai bakwai .
(trg)="s2.29.0"> Egli ha creato per voi tutto quello che c'è sulla terra .
(trg)="s2.29.1"> Poi si è rivolto al cielo e lo ha ordinato in sette cieli .
(src)="s2.29.1"> Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne .
(trg)="s2.29.2"> Egli è l' Onnisciente .
(src)="s2.30"> Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã 'iku : " Lalle ne , Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa , " suka ce : " Ashe , zã Ka sanya a cikinta , wanda zai yi ɓarna a cikinta , kuma mu , muna yi maka tasbihi tare da gõde maka , kuma muna tsarkakewa gareka " Ya ce : " Lalle ne , Ni Na san abin da ba ku sani ba . "
(trg)="s2.30.0"> E quando il tuo Signore disse agli Angeli : “ Porrò un vicario sulla terra” , essi dissero : “ Metterai su di essa qualcuno che vi spargerà la corruzione e vi verserà il sangue , mentre noi Ti glorifichiamo lodandoTi e Ti santifichiamo ?” .
(trg)="s2.30.1"> Egli disse : “ In verità , Io conosco quello che voi non conoscete ...” .
(src)="s2.31"> Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu , sa 'an nan kuma ya gitta su a kan malã 'iku , sa 'n nan Ya ce : " Ku gaya mini sũnayen waɗannan , idan kun nasance mãsu gaskiya . "
(trg)="s2.31"> Ed insegnò ad Adamo i nomi di tutte le cose , quindi le presentò agli Angeli e disse : “ Ditemi i loro nomi , se siete veritieri” .
(src)="s2.32.0"> Suka ce : " Tsarki ya tabbata a gare Ka !
(trg)="s2.32.0"> Essi dissero : “ Gloria a Te .
(src)="s2.32.1"> Bãbu sani a gare mu , lalle ne Kai , Kai ne Masani , Mai hikima . "
(trg)="s2.32.1"> Non conosciamo se non quello che Tu ci hai insegnato : in verità Tu sei il Saggio , il Sapiente” .
(src)="s2.33.0"> Ya ce : " Yã Ãdam !
(src)="s2.33.1"> Ka gaya musu sũnãyensu . "
(trg)="s2.33.0"> Disse : “ O Adamo , informali sui nomi di tutte [ le cose ]” .
(src)="s2.33.2"> To , a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu , ( Allah ) Ya ce : " Ashe , ban ce muku ba , lalle Ni , Inã sane da gaibin sammai da ƙasa , kuma ( Inã sane da ) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa ? "
(trg)="s2.33.1"> Dopo che li ebbe informati sui nomi , Egli disse : “ Non vi avevo forse detto che conosco il segreto dei cieli e della terra e che conosco ciò che manifestate e ciò che nascondete ?” .
(src)="s2.34"> Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã 'iku : " Ku yi sujada ga Ãdam , " Sai suka yi sujada , fãce Ibilĩsa ya ƙi , kuma ya yi girman kai , kuma ya kasance daga kãfirai .
(trg)="s2.34"> E quando dicemmo agli Angeli : “ Prosternatevi ad Adamo” , tutti si prosternarono , eccetto Iblîs , che rifiutò per orgoglio e fu tra i miscredenti .
(src)="s2.35.0"> Kuma muka ce : " Ya Ãdam !
(src)="s2.35.1"> Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna , kuma ku ci daga gare ta , bisa wadãta , inda kuke so , kuma kada ku kusanci wannan itãciyar , har ku kasance daga azzãlumai . "
(trg)="s2.35.0"> E dicemmo : “ O Adamo , abita il Paradiso , tu e la tua sposa .
(trg)="s2.35.1"> Saziatevene ovunque a vostro piacere , ma non avvicinatevi a quest' albero , ché in tal caso sareste tra gli empi” .
(src)="s2.36.0"> Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta , sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa .
(trg)="s2.36.0"> Poi Iblîs li fece inciampare e scacciare dal luogo in cui si trovavano .
(src)="s2.36.1"> Kuma muka ce : " Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe , kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci . "
(trg)="s2.36.1"> E Noi dicemmo : “ Andatevene via , nemici gli uni degli altri .
(trg)="s2.36.2"> Avrete una dimora sulla terra e ne godrete per un tempo stabilito” .
(src)="s2.37.0"> Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa , sabõda haka ya karɓi tũba a kansa .
(trg)="s2.37.0"> Adamo ricevette parole dal suo Signore e Allah accolse il suo [ pentimento ] .
(src)="s2.37.1"> Lalle ne Shi , Shĩ ne Mai karɓar tũba , Mai jin ƙai .
(trg)="s2.37.1"> In verità Egli è Colui Che accetta il pentimento , il Misericordioso .
(src)="s2.38.0"> Muka ce : " Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya .
(trg)="s2.38.0"> Dicemmo : “ Andatevene via tutti [ quanti ] !
(src)="s2.38.1"> To , imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni , to , wanda ya bi shiriya ta to , bãbu tsõro a kansu , kuma bã su yin baƙin ciki . "
(trg)="s2.38.1"> Se mai vi giungerà una guida da parte Mia , coloro che la seguiranno non avranno nulla da temere e non saranno afflitti” .
(src)="s2.39"> " Kuma waɗanda suka kãfirta , kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu , waɗannan sũ ne abõkan Wuta ; sũ a cikinta madawwama ne . "
(trg)="s2.39"> E i miscredenti che smentiscono i Nostri segni , sono i compagni del Fuoco , in cui rimarranno per sempre .
(src)="s2.40.0"> Yã Banĩ Isrã 'Ĩla !
(src)="s2.40.1"> Ku tuna ni 'imãTa a kanku , kuma ku cika alƙawariNa , In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni , ku ji tsõro Na .
(trg)="s2.40.0"> O figli di Israele , ricordate i favori di cui vi ho colmati e rispettate il Mio patto e rispetterò il vostro .
(trg)="s2.40.1"> Solo Me dovete temere .
(src)="s2.41.0"> Kuma , ku yi ĩmãni da abin da na saukar , mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku , kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi , Kuma kada ku sayi ' yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa .
(trg)="s2.41.0"> E credete in ciò che ho fatto scendere a conferma di quello che già era sceso su di voi e non siate i primi a rinnegarlo : non svendete i Miei segni per un prezzo vile .
(src)="s2.41.1"> Kuma ku ji tsõrõNa , Nĩ kaɗai .
(trg)="s2.41.1"> E temete soltanto Me .
(src)="s2.42"> Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya , kuma ku ɓõye gaskiya , alhãli kuwa kuna sane .
(trg)="s2.42"> E non avvolgete la verità di menzogna e non nascondete la verità ora che la conoscete .
(src)="s2.43"> Kuma ku tsayar da salla ; kuma ku bãyar da zakka ; kuma ku yi rukũ 'i tãre da mãsu yin rukũ 'i .
(trg)="s2.43"> E assolvete all' orazione , pagate la decima e inchinatevi con coloro che si inchinano .
(src)="s2.44.0"> Shin , kuna umurnin mutãne da alhẽri , kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi ?
(trg)="s2.44.0"> Ordinerete ai popoli la carità e dimenticherete voi stessi , voi che leggete il Libro ?
(src)="s2.44.1"> Shin , bãzã ku hankalta ba ?
(trg)="s2.44.1"> Non ragionate dunque ?
(src)="s2.45.0"> Kuma ku nẽmi taimako da yin haƙuri , da salla .
(src)="s2.45.1"> Kuma lalle ne ita , haƙĩƙa , mai girma ce fãce fa a kan mãsu tsõron Allah .
(trg)="s2.45"> Cercate aiuto nella pazienza e nell' adorazione , in verità essa è gravosa , ma non per gli umili
(src)="s2.46"> Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle ne su mãsu haɗuwa da Ubangijinsu , kuma lalle ne sũ a gareshi mãsu kõmãwa ne .
(trg)="s2.46"> che pensano che invero incontreranno il loro Signore e che invero torneranno a Lui .
(src)="s2.47.0"> Yã banĩ Isrã 'ĩla !
(src)="s2.47.1"> Ku tuna ni 'imaTa , wadda Na ni 'imta a kanku , kuma lalle ne Ni , na fĩfĩta ku a kan tãlikai .
(trg)="s2.47"> O Figli di Israele , ricordate i favori di cui vi ho colmati e di come vi ho favorito sugli altri popoli del mondo .
(src)="s2.48"> Kuma ku ji tsron wani yini , ( a cikinsa ) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme , kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi , kuma ba a karɓar fansa daga gare shi , kuma bã su zama ana taimakon su ba .
(trg)="s2.48.0"> E temete il Giorno in cui nessun'anima potrà alcunché per un' altra , in cui non sarà accolta nessuna intercessione e nulla potrà essere compensato .
(trg)="s2.48.1"> Essi non saranno soccorsi .
(src)="s2.49.0"> Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir 'auna , su na taya muku muguntar azãba , su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku .
(trg)="s2.49.0"> E [ ricordate ] quando vi abbiamo liberato dalla gente di Faraone che vi infliggeva le torture più atroci ! ...
(trg)="s2.49.1"> Sgozzavano i vostri figli e lasciavano in vita le vostre femmine .
(src)="s2.49.1"> Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku .
(trg)="s2.49.2"> In ciò vi fu un' immensa prova da [ parte del ] vostro Signore .
(src)="s2.50"> Kuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku , sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir 'auna , alhãli kuwa kũ kuna kallo .
(trg)="s2.50"> E quando abbiamo diviso il mare per voi , quindi vi abbiamo tratti in salvo e abbiamo annegato la gente di Faraone , mentre voi stavate a guardare .
(src)="s2.51"> Kuma a lõkacin da muka yi wa 'adi ga Mũsa , dare arba 'in , sa 'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa , alhãli kũ , kuna mãsu zãlunci ( da bauta masa ) .
(trg)="s2.51"> E quando stabilimmo con Mosè [ un patto in ] quaranta notti ... e voi vi prendeste il Vitello e agiste da iniqui .
(src)="s2.52"> Sa 'an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan , tsammãninku , kuna gõdẽwa .
(trg)="s2.52"> Ma Noi vi perdonammo : forse ne sareste stati riconoscenti .
(src)="s2.53"> Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabẽwa , tsammãninku , kuna shiryuwa .
(trg)="s2.53"> E quando abbiamo dato a Mosè il Libro e il Discrimine : forse sarete ben guidati !
(src)="s2.54.0"> Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa : " Ya mutãnena !
(trg)="s2.54.0"> E quando Mosè disse al suo popolo : “ O popol mio , invero vi siete fatti un grande torto prendendovi il Vitello .
(src)="s2.54.1"> Lalle ne ku , kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin , sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku , sai ku kashe kãwunanku .
(trg)="s2.54.1"> Pentitevi al vostro Creatore e datevi la morte : questa è la cosa migliore , di fronte al vostro Creatore” .
(src)="s2.54.2"> Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku .
(trg)="s2.54.2"> Poi Allah accolse il vostro [ pentimento ] .
(src)="s2.54.3"> Sa 'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi , Shi ne Mai karɓar tũba , Mai jin ƙai .
(trg)="s2.54.3"> In verità Egli accoglie sempre [ il pentimento ] , è il Misericordioso
(src)="s2.55.0"> Kuma a lõkacin da kuka ce : " Ya Musa !
(src)="s2.55.1"> Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka , sai munga Allah bayyane , " sabada haka tsãwar nan ta kamaku , alhãli kuwa kuna kallo .
(trg)="s2.55.0"> E quando diceste : “ O Mosè , noi non ti crederemo finché non avremo visto Allah in maniera evidente” .
(trg)="s2.55.1"> E la folgore vi colpì mentre stavate guardando .
(src)="s2.56"> Sa 'an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku , tsammãninku , kuna gõdẽwa .
(trg)="s2.56"> Poi vi resuscitammo dalla morte : forse sarete riconoscenti .
(src)="s2.57"> Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku , kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku ; " Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku . " kuma ba su zãlunce Mu ba , kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta .
(trg)="s2.57.0"> E vi coprimmo con l' ombra di una nuvola , e facemmo scendere su di voi la manna e le quaglie : “ Mangiate queste delizie di cui vi abbiamo provvisti !” .
(trg)="s2.57.1"> Non è a Noi che fecero torto , bensì a loro stessi .
(src)="s2.58.0"> Kuma a lokacin da Muka ce : " Ku shiga wannan alƙarya .
(src)="s2.58.1"> San nan ku ci daga gareta , idan kuka so , bisa wadata , kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu 'i , kuma ku ce ; " kãyar da zunubai " Mu gãfarta muku laifukanku , kuma zã mu ƙãra wa mãsu kyautatawa . "
(trg)="s2.58.0"> E quando dicemmo : “ Entrate in questa città e rifocillatevi dove volete a vostro piacimento ; ma entrate dalla porta inchinandovi e dicendo " perdono " .
(trg)="s2.58.1"> Noi perdoneremo i vostri peccati ed aumenteremo coloro che avranno operato il bene” .
(src)="s2.59"> Sai waɗanda suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu , saboda haka muka saukar a kan waɗanda suka yi zãlunci da azãba daga sama sabõda abin da suka kasance suna yi na fãsiƙanci .
(trg)="s2.59.0"> Ma gli empi cambiarono la parola che era stata data loro .
(trg)="s2.59.1"> E facemmo scendere dal cielo un castigo sugli empi , per castigare la loro perversione .
(src)="s2.60.0"> Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa , Muka ce ; " Ka dõki dũtsen da sandarka . "
(trg)="s2.60.0"> E quando Mosè chiese acqua per il suo popolo , dicemmo : “ Colpisci la roccia con il tuo bastone” .
(src)="s2.60.1"> Sai marmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓugo , haƙĩƙa , kõwaɗanne mutãne sun san wurin shansu .
(trg)="s2.60.1"> E , improvvisamente , sgorgarono dodici fonti , e ogni tribù seppe dove doveva bere !
(src)="s2.60.2"> " Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku , kuma kada ku yi fasadi , a cikin ƙasa , kuna mãsu ɓarna . "
(trg)="s2.60.2">“ Mangiate e bevete il sostentamento di Allah e non spargete la corruzione sulla terra .”
(src)="s2.61.0"> Kuma a lõkacin da kuka ce : " Yã Mũsã !
(src)="s2.61.1"> Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda .
(trg)="s2.61.0"> E quando diceste : “ O Mosè , non possiamo più tollerare un unico alimento .
(src)="s2.61.2"> Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta , dumanta , da alkamarta da albasarta .
(trg)="s2.61.1"> Prega per noi il tuo Signore che , dalla terra , faccia crescere per noi legumi , cetrioli , aglio , lenticchie e cipolle !” .
(src)="s2.61.3"> Ya ce : " Kuna nẽman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhẽri ?
(trg)="s2.61.2"> Egli disse : “ Volete scambiare il meglio con il peggio ?
(src)="s2.61.4"> Ku sauka wani birni ( daga cikin birane ) , lalle ne , kuna da abin da kuka rõƙa .
(src)="s2.61.5"> " Kuma Muka dõka musu walãƙanci da talauci .
(trg)="s2.61.3"> Tornate in Egitto , colà troverete certamente quello che chiedete !” .
(src)="s2.61.6"> Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah .
(src)="s2.61.7"> Wancan sabõda lalle su , sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah , kuma suna kashe Aannabãwa , bãda hakki ba .
(trg)="s2.61.4"> E furono colpiti dall' abiezione e dalla miseria e subirono la collera di Allah , perché dissimulavano i segni di Allah e uccidevano i profeti ingiustamente .
(src)="s2.61.8"> Wancan , sabõda sãɓawarsu ne , kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi .
(trg)="s2.61.5"> Questo perché disobbedivano e trasgredivano .
(src)="s2.62"> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni , da waɗanda suka tũba , da Nasãra da Makarkata , wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira , kuma ya aikata aikin ƙwarai , to , suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu , kuma bãbu tsõro a kansu , kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba .
(trg)="s2.62.0"> In verità , coloro che credono , siano essi giudei , nazareni o sabei , tutti coloro che credono in Allah e nell' Ultimo Giorno e compiono il bene riceveranno il compenso presso il loro Signore .
(trg)="s2.62.1"> Non avranno nulla da temere e non saranno afflitti .
(src)="s2.63.0"> Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku , kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku : " Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi .
(trg)="s2.63.0"> E quando stringemmo il Patto con voi ed elevammo il Monte : “ Tenetevi saldi a quello che vi abbiamo dato e ricordatevi di quello che contiene !” .
(src)="s2.63.1"> Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa , tsammãninku ku kãrekanku .
(trg)="s2.63.1"> Forse potrete essere timorati !
(src)="s2.64"> Sa 'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan , to , bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku , haƙĩƙa , dã kun kasance daga mãsu hasãra . "
(trg)="s2.64"> Ma poi volgeste le spalle , e senza la grazia di Allah e la Sua misericordia per voi , sareste certamente stati tra i perdenti .
(src)="s2.65"> Kuma lalle ne , haƙĩƙa , kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar , sai muka ce musu : " ku kasance birai ƙasƙantattu . "
(trg)="s2.65"> Avrete saputo di quelli dei vostri che trasgredirono il Sabato ai quali dicemmo : “ Siate scimmie reiette” .