# es/cortes.xml.gz
# ha/gumi.xml.gz


(src)="s1.1"> ¡ En el nombre de Alá , el Compasivo , el Misericordioso !
(trg)="s1.1"> Da sũnan Allah , Mai rahama , Mai jin ƙai .

(src)="s1.2"> Alabado sea Alá , Señor del universo ,
(trg)="s1.2"> Godiya ta tabbata ga Allah , Ubangijin halittu ;

(src)="s1.3"> el Compasivo , el Misericordioso ,
(trg)="s1.3"> Mai rahama , Mai jin ƙai ;

(src)="s1.4"> Dueño del día del Juicio ,
(trg)="s1.4"> Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako .

(src)="s1.5"> A Ti solo servimos y a Ti solo imploramos ayuda .
(trg)="s1.5"> Kai muke bauta wa , kuma Kai muke neman taimakonKa .

(src)="s1.6"> Dirígenos por la vía recta ,
(trg)="s1.6"> Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya .

(src)="s1.7"> la vía de los que Tú has agraciado , no de los que han incurrido en la ira , ni de los extraviados .
(trg)="s1.7"> Hanyar waɗanda Ka yi wa ni 'ima , ba waɗanda aka yi wa fushi ba , kuma ba ɓatattu ba .

(src)="s2.1"> ` lm .
(trg)="s2.1.0"> A. L ̃ .
(trg)="s2.1.1"> M ̃ .

(src)="s2.2"> Ésta es la Escritura , exenta de dudas , como dirección para los temerosos de Alá ,
(trg)="s2.2"> Wãncan ne Littãfi , bãbu shakka a cikinsa , shiriya ne ga mãsu taƙawa .

(src)="s2.3"> que creen en lo oculto , hacen la azalá y dan limosna de lo que les hemos proveído .
(trg)="s2.3"> Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi , kuma suna tsayar da salla , kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa .

(src)="s2.4"> creen en lo que se te ha revelado a ti y antes de ti , y están convencidos de la otra vida .
(trg)="s2.4"> Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka , da abin da aka saukar daga gabãninka , kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni .

(src)="s2.5"> Ésos son los dirigidos por su Señor y ésos los que prosperarán .
(trg)="s2.5"> Waɗannan suna kan shiriya , daga Ubangjinsu , kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara .

(src)="s2.6"> Da lo mismo que adviertas o no a los infieles : no creen .
(trg)="s2.6"> Lalle ne waɗanda suka kãfirta daidai ne a kansu , shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba , ba zã su yi ĩmãni ba .

(src)="s2.7"> Alá ha sellado sus corazones y oídos ; una venda cubre sus ojos y tendrán un castigo terrible .
(trg)="s2.7"> Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu , da a kan jinsu , kuma a Kan ganin su akwai wata yãna ; kuma suna da wata azãba mai girma .

(src)="s2.8"> Hay entre los hombres quienes dicen : « Creemos en Alá y en el último Día » , pero no creen .
(trg)="s2.8.0"> Kuma akwai daga mutãne wanda yake cewa : " Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira . "
(trg)="s2.8.1"> Alhãli kuwa su ba muminai ba ne .

(src)="s2.9"> Tratan de engañar a Alá y a los que creen ; pero , sin darse cuenta , sólo se engañan a sí mismos .
(trg)="s2.9"> Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni , alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu , kuma bã su sakankancẽwa !

(src)="s2.10.0"> Sus corazones están enfermos y Alá les ha agravado su enfermedad .
(src)="s2.10.1"> Tendrán un castigo doloroso por haber mentido .
(trg)="s2.10.0"> A cikin zukãtansu akwai wata cũta .
(trg)="s2.10.1"> Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta , kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya .

(src)="s2.11"> Cuando se les dice : « ¡ No corrompáis en la tierra ! » , dicen : « Pero ¡ si somos reformadores ! »
(trg)="s2.11"> Kuma idan aka ce musu : " Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa , " sukan ce : " Mũ mãsu kyautatawa kawai ne ! "

(src)="s2.12.0"> ¡ No son ellos , en realidad , los corruptores ?
(src)="s2.12.1"> Pero no se dan cuenta .
(trg)="s2.12"> To , lalle ne su , sũne mãsu ɓarna , kuma amma bã su sansancewa .

(src)="s2.13.0"> Cuando se les dice : « ¡ Creed como creen los demás ! » , dicen : « ¿ Es que vamos a creer como creen los tontos ? »
(trg)="s2.13.0"> Kuma idan aka ce musu : " ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni , " sukan ce : " Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni ? "

(src)="s2.13.1"> Son ellos los tontos , pero no lo saben .
(trg)="s2.13.1"> To , lalle ne su , sũ ne wãwãye , kuma amma bã su sani .

(src)="s2.14.0"> Cuando encuentran a quienes creen , dicen : « ¡ Creemos ! »
(trg)="s2.14.0"> Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni , sukan ce : " Mun yi ĩmãni .

(src)="s2.14.1"> Pero , cuando están a solas con sus demonios , dicen : « Estamos con vosotros , era sólo una broma » .
(trg)="s2.14.1"> " Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu , sukan ce : " Lalle ne muna tãre da ku : Mu mãsu izgili , kawai ne . "

(src)="s2.15"> Alá les devolverá la broma y les dejará que persistan en su rebeldía , errando ciegos .
(trg)="s2.15"> Allah Yana yin izgili gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu , suna ɗimuwa .

(src)="s2.16.0"> Ésos son los que han trocado la Dirección por el extravío .
(src)="s2.16.1"> Por eso , su negocio no ha resultado lucrativo y no han sido bien dirigidos .
(trg)="s2.16"> Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya , sai fataucinsu bai yi rĩba ba , kuma ba su kasance masu shiryuwa ba .

(src)="s2.17.0"> Son como uno que alumbra un fuego .
(src)="s2.17.1"> En cuanto éste ilumina lo que le rodea , Alá se les lleva la luz y les deja en tinieblas : no ven .
(trg)="s2.17"> Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta , to , a lõkacin da ta haskake abin da yake gẽfensa ( na abin tsõro ) , Allah Ya tafi da haskensu , kuma Ya bar su a cikin duffai , bã su gani .

(src)="s2.18"> Son sordos , mudos , ciegos , no se convierten .
(trg)="s2.18"> Kurãme , bẽbãye , makãfi , sabõda haka bã su kõmõwa .

(src)="s2.19.0"> O como si viniera del cielo una nube borrascosa , cargada de tinieblas , truenos y relámpagos .
(src)="s2.19.1"> Se ponen los dedos en los oídos contra el rayo , por temor a la muerte .
(trg)="s2.19.0"> Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama , a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya : suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin , dõmin tsõron mutuwa .

(src)="s2.19.2"> Pero Alá cerca a los infieles .
(trg)="s2.19.1"> Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai !

(src)="s2.20.0"> El relámpago les arrebata casi la vista .
(src)="s2.20.1"> Cuando les ilumina , caminan a su luz ; pero , cuando les oscurece , se detienen .
(trg)="s2.20.0"> Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu , ko da yaushe ta haskakã musu , sai su yi tafiya a cikinta , kuma idan ta yi duhu a kansu , sai su yi tsaye .

(src)="s2.20.2"> Si Alá hubiera querido , les habría quitado el oído y la vista .
(trg)="s2.20.1"> Kuma dã Allah Yã so , sai Ya tafi da jinsu da gannansu .

(src)="s2.20.3"> Alá es omnipotente .
(trg)="s2.20.2"> Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne .

(src)="s2.21.0"> ¡ Hombres !
(trg)="s2.21.0"> Yã ku mutãne !

(src)="s2.21.1"> Servid a vuestro Señor , Que os ha creado , a vosotros y a quienes os precedieron .
(src)="s2.21.2"> Quizás , así , tengáis temor de Él .
(trg)="s2.21.1"> Ku bauta wa Ubangjinku , Wanda Ya halicce ku , kũ da waɗanda suke daga gabãninku , tsammãninku ku kãre kanku !

(src)="s2.22.0"> Os ha hecho de la tierra lecho y del cielo edificio .
(src)="s2.22.1"> Ha hecho bajar agua del cielo , mediante la cual ha sacado frutos para sustentaros .
(trg)="s2.22.0"> Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa , kuma sama gini , kuma Ya saukar da ruwa daga sama , sa 'an nan Ya fitar da abinci daga ' ya 'yan itãce game da shi , sabõda ku .

(src)="s2.22.2"> No atribuyáis iguales a Alá a sabiendas .
(trg)="s2.22.1"> Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi , alhãli kuwa kuna sane .

(src)="s2.23"> Si dudáis de lo que hemos revelado a Nuestro siervo , traed una sura semejante y , si es verdad lo que decís , llamad a vuestros testigos en lugar de llamar a Alá .
(trg)="s2.23.0"> Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bãwanmu , to , ku zõ da sũra guda daga misalinsa ( Alƙur 'ãni ) .
(trg)="s2.23.1"> Kuma ku kirãwo shaidunku baicin Allah , idan kun kasance mãsu gaskiya .

(src)="s2.24"> Pero , si no lo hacéis -y nunca podréis hacerlo- , guardaos del fuego cuyo combustible lo constituyen hombres y piedras , y que ha sido preparado para los infieles .
(trg)="s2.24"> To , idan ba ku aikata ( kãwo sura ) ba , to , bã zã ku aikataba , sabõda haka , ku ji tsoron wuta , wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne , an yi tattalinta dõmin kãfurai .

(src)="s2.25.0"> Anuncia la buena nueva a quienes creen y obran bien : tendrán jardines por cuyos bajos fluyen arroyos .
(src)="s2.25.1"> Siempre que se les dé como sustento algún fruto de ellos , dirán : « Esto es igual que lo que se nos ha dado antes » .
(trg)="s2.25.0"> Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai , cẽwa lallene , suna da gidãjen Aljanna , ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu .

(src)="s2.25.2"> Pero se les dará algo sólo parecido .
(src)="s2.25.3"> Tendrán esposas purificadas y estarán allí eternamente .
(trg)="s2.25.1"> Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu ' ya 'yan itãce daga gare su , sai su ce : " Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka , " Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna , Kuma sunã da , a cikin su , mãtan aure mãsu tsarki , kuma su , cikin su madawwama ne .

(src)="s2.26.0"> Alá no se avergüenza de proponer la parábola que sea , aunque se trate de un mosquito .
(src)="s2.26.1"> Los que creen saben que es la Verdad , que viene de su Señor .
(src)="s2.26.2"> En cuanto a los que no creen , dicen : « ¿ Qué es lo que se propone Alá con esta parábola ? »
(src)="s2.26.3"> Así extravía Él a muchos y así también dirige a muchos .
(src)="s2.26.4"> Pero no extravía así sino a los perversos .
(trg)="s2.26.0"> Lalle ne , Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli , kõwane iri ne , sauro da abin da yake bisa gare shi .
(trg)="s2.26.1"> To , amma waɗanda suka yi ĩmãni , sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su , kuma amma waɗanda suka kãfirta , sai su ce : " Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan ya zama misãli ? " na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi , kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi , kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai .

(src)="s2.27"> Quienes violan la alianza con Alá después de haberla concluido , cortan los lazos que Alá ha ordenado mantener y corrompen en la tierra , ésos son los que pierden .
(trg)="s2.27"> Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi , kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sãdar , kuma suna ɓarna a cikin ƙasa , waɗannan sũ ne mãsu hasãra .

(src)="s2.28"> ¿ Cómo podéis no creer en Alá , siendo así que os dio la vida cuando aún no existíais , que os hará morir y os volverá a la vida , después de lo cual seréis devueltos a Él ?
(trg)="s2.28"> Yaya kuke kãfirta da Allah , alhãli kuwa kun kasance matattu sa 'an nan Ya rãyar da ku , sa 'nnan kuma Ya matar da ku , sa 'an nan kuma Ya rãya ku , sa 'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku ?

(src)="s2.29.0"> Él es Quien creó para vosotros cuanto hay en la tierra .
(src)="s2.29.1"> Y subió al cielo e hizo de él siete cielos .
(trg)="s2.29.0"> Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya , sa 'an nan kuma Ya daidaita zuwa sama , sa 'an nan Y a aikata su sammai bakwai .

(src)="s2.29.2"> Es omnisciente .
(trg)="s2.29.1"> Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne .

(src)="s2.30.0"> Y cuando tu Señor dijo a los ángeles : « Voy a poner un sucesor en la tierra » .
(src)="s2.30.1"> Dijeron : « ¿ Vas a poner en ella a quien corrompa en ella y derrame sangre , siendo así que nosotros celebramos Tu alabanza y proclamamos Tu santidad ? »
(src)="s2.30.2"> Dijo : « Yo sé lo que vosotros no sabéis » .
(trg)="s2.30"> Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã 'iku : " Lalle ne , Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa , " suka ce : " Ashe , zã Ka sanya a cikinta , wanda zai yi ɓarna a cikinta , kuma mu , muna yi maka tasbihi tare da gõde maka , kuma muna tsarkakewa gareka " Ya ce : " Lalle ne , Ni Na san abin da ba ku sani ba . "

(src)="s2.31"> Enseñó a Adán los nombres de todos los seres y presentó éstos a los ángeles diciendo : « Informadme de los nombres de éstos , si es verdad lo que decís » .
(trg)="s2.31"> Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu , sa 'an nan kuma ya gitta su a kan malã 'iku , sa 'n nan Ya ce : " Ku gaya mini sũnayen waɗannan , idan kun nasance mãsu gaskiya . "

(src)="s2.32.0"> Dijeron : « ¡ Gloria a Ti !
(trg)="s2.32.0"> Suka ce : " Tsarki ya tabbata a gare Ka !

(src)="s2.32.1"> No sabemos más que lo que Tú nos has enseñado .
(src)="s2.32.2"> Tú eres , ciertamente , el Omnisciente , el Sabio » .
(trg)="s2.32.1"> Bãbu sani a gare mu , lalle ne Kai , Kai ne Masani , Mai hikima . "

(src)="s2.33.0"> Dijo : « ¡ Adán !
(trg)="s2.33.0"> Ya ce : " Yã Ãdam !

(src)="s2.33.1"> ¡ Infórmales de sus nombres ! »
(trg)="s2.33.1"> Ka gaya musu sũnãyensu . "

(src)="s2.33.2"> Cuando les informó de sus nombres , dijo : « ¿ No os he dicho que conozco lo oculto de los cielos y de la tierra y que sé lo que mostráis lo que ocultáis ? »
(trg)="s2.33.2"> To , a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu , ( Allah ) Ya ce : " Ashe , ban ce muku ba , lalle Ni , Inã sane da gaibin sammai da ƙasa , kuma ( Inã sane da ) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa ? "

(src)="s2.34.0"> Y cuando dijimos a los ángeles : « ¡ Prosternaos ante Adán ! » .
(src)="s2.34.1"> Se prosternaron , excepto Iblis .
(src)="s2.34.2"> Se negó y fue altivo : era de los infieles .
(trg)="s2.34"> Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã 'iku : " Ku yi sujada ga Ãdam , " Sai suka yi sujada , fãce Ibilĩsa ya ƙi , kuma ya yi girman kai , kuma ya kasance daga kãfirai .

(src)="s2.35.0"> Dijimos : « ¡ Adán !
(trg)="s2.35.0"> Kuma muka ce : " Ya Ãdam !

(src)="s2.35.1"> ¡ Habita con tu esposa en el Jardín y comed de él cuanto y donde queráis . pero no os acerquéis a este árbol !
(src)="s2.35.2"> Si no , seréis de los impíos » .
(trg)="s2.35.1"> Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna , kuma ku ci daga gare ta , bisa wadãta , inda kuke so , kuma kada ku kusanci wannan itãciyar , har ku kasance daga azzãlumai . "

(src)="s2.36.0"> Pero el Demonio les hizo caer , perdiéndolo , y les sacó del estado en que estaban .
(src)="s2.36.1"> Y dijimos : « ¡ Descended !
(trg)="s2.36.0"> Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta , sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa .

(src)="s2.36.2"> Seréis enemigos unos de otros .
(src)="s2.36.3"> La tierra será por algún tiempo vuestra morada y lugar de disfrute » .
(trg)="s2.36.1"> Kuma muka ce : " Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe , kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci . "

(src)="s2.37.0"> Adán recibió palabras de su Señor y Éste se volvió a él .
(trg)="s2.37.0"> Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa , sabõda haka ya karɓi tũba a kansa .

(src)="s2.37.1"> Él es el Indulgente , el Misericordioso .
(trg)="s2.37.1"> Lalle ne Shi , Shĩ ne Mai karɓar tũba , Mai jin ƙai .

(src)="s2.38.0"> Dijimos : « ¡ Descended todos de él !
(trg)="s2.38.0"> Muka ce : " Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya .

(src)="s2.38.1"> Si . pues , recibís de Mí una dirección , quienes sigan Mi dirección no tendrán que . temer y no estarán tristes .
(trg)="s2.38.1"> To , imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni , to , wanda ya bi shiriya ta to , bãbu tsõro a kansu , kuma bã su yin baƙin ciki . "

(src)="s2.39"> Pero quienes no crean y desmientan Nuestros signos , ésos morarán en el Fuego eternamente » .
(trg)="s2.39"> " Kuma waɗanda suka kãfirta , kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu , waɗannan sũ ne abõkan Wuta ; sũ a cikinta madawwama ne . "

(src)="s2.40.0"> ¡ Hijos de Israel !
(trg)="s2.40.0"> Yã Banĩ Isrã 'Ĩla !

(src)="s2.40.1"> Recordad la gracia que os dispensé y sed fieles a la alianza que conmigo concluisteis .
(src)="s2.40.2"> Entonces , Yo seré fiel a la que con vosotros concluí .
(trg)="s2.40.1"> Ku tuna ni 'imãTa a kanku , kuma ku cika alƙawariNa , In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni , ku ji tsõro Na .

(src)="s2.41.0"> ¡ Creed en lo que he revelado en confirmación de lo que habéis recibido !
(src)="s2.41.1"> ¡ No seáis los primeros en no creer en ello , ni malvendáis Mis signos !
(trg)="s2.41.0"> Kuma , ku yi ĩmãni da abin da na saukar , mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku , kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi , Kuma kada ku sayi ' yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa .

(src)="s2.41.2"> ¡ Temedme , pues , a Mí . y sólo a Mí !
(trg)="s2.41.1"> Kuma ku ji tsõrõNa , Nĩ kaɗai .

(src)="s2.42"> ¡ No disfracéis la Verdad de falsedad , ni ocultéis la Verdad conociéndola !
(trg)="s2.42"> Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya , kuma ku ɓõye gaskiya , alhãli kuwa kuna sane .

(src)="s2.43"> ¡ Haced la azalá , dad el azaque e inclinaos con los que se inclinan !
(trg)="s2.43"> Kuma ku tsayar da salla ; kuma ku bãyar da zakka ; kuma ku yi rukũ 'i tãre da mãsu yin rukũ 'i .

(src)="s2.44.0"> ¿ Mandáis a los hombres que sean piadosos y os olvidáis de vosotros mismos siendo así que leéis la Escritura ?
(trg)="s2.44.0"> Shin , kuna umurnin mutãne da alhẽri , kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi ?

(src)="s2.44.1"> ¿ Es que no tenéis entendimiento ?
(trg)="s2.44.1"> Shin , bãzã ku hankalta ba ?

(src)="s2.45.0"> ¡ Buscad ayuda en la paciencia y en la azalá !
(trg)="s2.45.0"> Kuma ku nẽmi taimako da yin haƙuri , da salla .

(src)="s2.45.1"> Sí , es algo difícil , pero no para los humildes ,
(trg)="s2.45.1"> Kuma lalle ne ita , haƙĩƙa , mai girma ce fãce fa a kan mãsu tsõron Allah .

(src)="s2.46"> que cuentan con encontrar a su Señor y volver a Él .
(trg)="s2.46"> Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle ne su mãsu haɗuwa da Ubangijinsu , kuma lalle ne sũ a gareshi mãsu kõmãwa ne .

(src)="s2.47.0"> ¡ Hijos de Israel !
(trg)="s2.47.0"> Yã banĩ Isrã 'ĩla !

(src)="s2.47.1"> Recordad la gracia que os dispensé y que os distinguí entre todos los pueblos .
(trg)="s2.47.1"> Ku tuna ni 'imaTa , wadda Na ni 'imta a kanku , kuma lalle ne Ni , na fĩfĩta ku a kan tãlikai .

(src)="s2.48"> Temed un día en que nadie pueda satisfacer nada por otro , ni se acepte la intercesión ajena , compensación ni auxilio .
(trg)="s2.48"> Kuma ku ji tsron wani yini , ( a cikinsa ) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme , kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi , kuma ba a karɓar fansa daga gare shi , kuma bã su zama ana taimakon su ba .

(src)="s2.49.0"> Y cuando os salvamos de las gentes de Faraón , que os sometían a duro castigo , degollando a vuestros hijos varones y dejando con vida a vuestras mujeres .
(trg)="s2.49.0"> Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir 'auna , su na taya muku muguntar azãba , su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku .

(src)="s2.49.1"> Con esto os probó vuestro Señor duramente .
(trg)="s2.49.1"> Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku .

(src)="s2.50"> Y cuando os separamos las aguas del mar y os salvamos , anegando a las gentes de Faraón en vuestra presencia .
(trg)="s2.50"> Kuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku , sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir 'auna , alhãli kuwa kũ kuna kallo .

(src)="s2.51.0"> Y cuando nos dimos cita con Moisés durante cuarenta días .
(src)="s2.51.1"> Luego , cuando se fue , cogisteis el ternero , obrando impíamente .
(trg)="s2.51"> Kuma a lõkacin da muka yi wa 'adi ga Mũsa , dare arba 'in , sa 'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa , alhãli kũ , kuna mãsu zãlunci ( da bauta masa ) .

(src)="s2.52.0"> Luego , después de eso , os perdonamos .
(src)="s2.52.1"> Quizás , así , fuerais agradecidos .
(trg)="s2.52"> Sa 'an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan , tsammãninku , kuna gõdẽwa .

(src)="s2.53.0"> Y cuando dimos a Moisés la Escritura y el Criterio .
(src)="s2.53.1"> Quizás , así , fuerais bien dirigidos .
(trg)="s2.53"> Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabẽwa , tsammãninku , kuna shiryuwa .

(src)="s2.54.0"> Y cuando Moisés dijo a su pueblo : ¡ Pueblo !
(trg)="s2.54.0"> Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa : " Ya mutãnena !

(src)="s2.54.1"> Habéis sido injustos con vosotros mismos al coger el ternero .
(src)="s2.54.2"> ¡ Volveos a vuestro Creador y mataos unos a otros . !
(trg)="s2.54.1"> Lalle ne ku , kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin , sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku , sai ku kashe kãwunanku .

(src)="s2.54.3"> Esto es mejor para vosotros a los ojos de vuestro Creador .
(trg)="s2.54.2"> Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku .

(src)="s2.54.4"> Así se aplacará .
(src)="s2.54.5"> Él es el Indulgente , el Misericordioso » .
(trg)="s2.54.3"> Sa 'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi , Shi ne Mai karɓar tũba , Mai jin ƙai .

(src)="s2.55.0"> Y cuando dijisteis : « ¡ Moisés !
(trg)="s2.55.0"> Kuma a lõkacin da kuka ce : " Ya Musa !

(src)="s2.55.1"> No creeremos en ti hasta que veamos a Alá claramente » .
(src)="s2.55.2"> Y el Rayo se os llevó , viéndolo vosotros venir .
(trg)="s2.55.1"> Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka , sai munga Allah bayyane , " sabada haka tsãwar nan ta kamaku , alhãli kuwa kuna kallo .

(src)="s2.56.0"> Luego , os resucitamos después de muertos .
(src)="s2.56.1"> Quizás , así , fuerais agradecidos .
(trg)="s2.56"> Sa 'an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku , tsammãninku , kuna gõdẽwa .

(src)="s2.57.0"> Hicimos que se os nublara y que descendieran sobre vosotros el maná y las codornices : « ¡ Comed de las cosas buenas de que os hemos proveído ! »
(src)="s2.57.1"> No fueron injustos con Nosotros , sino que lo fueron consigo mismos .
(trg)="s2.57"> Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku , kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku ; " Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku . " kuma ba su zãlunce Mu ba , kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta .

(src)="s2.58.0"> Y cuando dijimos : « ¡ Entrad en esta ciudad , y comed donde y cuando queráis de lo que en ella haya !
(trg)="s2.58.0"> Kuma a lokacin da Muka ce : " Ku shiga wannan alƙarya .

(src)="s2.58.1"> ¡ Entrad por la puerta prosternándoos y decid '¡Perdón ! ' »
(src)="s2.58.2"> Os perdonaremos vuestros pecados y daremos más a quienes hagan el bien .
(trg)="s2.58.1"> San nan ku ci daga gareta , idan kuka so , bisa wadata , kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu 'i , kuma ku ce ; " kãyar da zunubai " Mu gãfarta muku laifukanku , kuma zã mu ƙãra wa mãsu kyautatawa . "

(src)="s2.59"> Pero los impíos cambiaron por otras las palabras que se les habían dicho e hicimos bajar contra los impíos un castigo del cielo por haber obrado perversamente .
(trg)="s2.59"> Sai waɗanda suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu , saboda haka muka saukar a kan waɗanda suka yi zãlunci da azãba daga sama sabõda abin da suka kasance suna yi na fãsiƙanci .

(src)="s2.60.0"> Y cuando Moisés pidió agua para su pueblo .
(src)="s2.60.1"> Dijimos : « ¡ Golpea la roca con tu vara ! »
(trg)="s2.60.0"> Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa , Muka ce ; " Ka dõki dũtsen da sandarka . "

(src)="s2.60.2"> Y brotaron de ella doce manantiales .
(src)="s2.60.3"> Todos sabían de cuál debían beber .
(trg)="s2.60.1"> Sai marmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓugo , haƙĩƙa , kõwaɗanne mutãne sun san wurin shansu .

(src)="s2.60.4"> « ¡ Comed y bebed del sustento de Alá y no obréis mal en la tierra corrompiendo ! »
(trg)="s2.60.2"> " Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku , kuma kada ku yi fasadi , a cikin ƙasa , kuna mãsu ɓarna . "

(src)="s2.61.0"> Y cuando dijisteis : « ¡ Moisés !
(trg)="s2.61.0"> Kuma a lõkacin da kuka ce : " Yã Mũsã !

(src)="s2.61.1"> No podremos soportar una sola clase de alimento .
(trg)="s2.61.1"> Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda .

(src)="s2.61.2"> ¡ Pide a tu Señor de parte nuestra que nos saque algo de lo que la tierra produce : verduras , pepinos , ajos , lentejas y cebollas ! »
(trg)="s2.61.2"> Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta , dumanta , da alkamarta da albasarta .