# en/ahmedali.xml.gz
# ha/gumi.xml.gz


(src)="s1.1"> In the name of Allah , most benevolent , ever-merciful .
(trg)="s1.1"> Da sũnan Allah , Mai rahama , Mai jin ƙai .

(src)="s1.2"> ALL PRAISE BE to Allah , Lord of all the worlds ,
(trg)="s1.2"> Godiya ta tabbata ga Allah , Ubangijin halittu ;

(src)="s1.3"> Most beneficent , ever-merciful ,
(trg)="s1.3"> Mai rahama , Mai jin ƙai ;

(src)="s1.4"> King of the Day of Judgement .
(trg)="s1.4"> Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako .

(src)="s1.5"> You alone we worship , and to You alone turn for help .
(trg)="s1.5"> Kai muke bauta wa , kuma Kai muke neman taimakonKa .

(src)="s1.6"> Guide us ( O Lord ) to the path that is straight ,
(trg)="s1.6"> Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya .

(src)="s1.7"> The path of those You have blessed , Not of those who have earned Your anger , nor those who have gone astray .
(trg)="s1.7"> Hanyar waɗanda Ka yi wa ni 'ima , ba waɗanda aka yi wa fushi ba , kuma ba ɓatattu ba .

(src)="s2.1"> ALIF LAM MIM .
(trg)="s2.1.0"> A. L ̃ .
(trg)="s2.1.1"> M ̃ .

(src)="s2.2"> This is The Book free of doubt and involution , a guidance for those who preserve themselves from evil and follow the straight path ,
(trg)="s2.2"> Wãncan ne Littãfi , bãbu shakka a cikinsa , shiriya ne ga mãsu taƙawa .

(src)="s2.3"> Who believe in the Unknown and fulfil their devotional obligations , and spend in charity of what We have given them ;
(trg)="s2.3"> Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi , kuma suna tsayar da salla , kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa .

(src)="s2.4"> Who believe in what has been revealed to you and what was revealed to those before you , and are certain of the Hereafter .
(trg)="s2.4"> Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka , da abin da aka saukar daga gabãninka , kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni .

(src)="s2.5"> They have found the guidance of their Lord and will be successful .
(trg)="s2.5"> Waɗannan suna kan shiriya , daga Ubangjinsu , kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara .

(src)="s2.6"> As for those who deny , it is all the same if you warn them or not , they will not believe .
(trg)="s2.6"> Lalle ne waɗanda suka kãfirta daidai ne a kansu , shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba , ba zã su yi ĩmãni ba .

(src)="s2.7.0"> God has sealed their hearts and ears , and veiled their eyes .
(src)="s2.7.1"> For them is great deprivation .
(trg)="s2.7"> Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu , da a kan jinsu , kuma a Kan ganin su akwai wata yãna ; kuma suna da wata azãba mai girma .

(src)="s2.8"> And there are some who , though they say : " We believe in God and the Last Day , " ( in reality ) do not believe .
(trg)="s2.8.0"> Kuma akwai daga mutãne wanda yake cewa : " Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira . "
(trg)="s2.8.1"> Alhãli kuwa su ba muminai ba ne .

(src)="s2.9"> They ( try to ) deceive God and those who believe , yet deceive none but themselves although they do not know .
(trg)="s2.9"> Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni , alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu , kuma bã su sakankancẽwa !

(src)="s2.10.0"> Sick are their hearts , and God adds to their malady .
(src)="s2.10.1"> For them is suffering for they lie .
(trg)="s2.10.0"> A cikin zukãtansu akwai wata cũta .
(trg)="s2.10.1"> Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta , kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya .

(src)="s2.11"> When asked to desist from spreading corruption in the land they say : " Why , we are reformers . "
(trg)="s2.11"> Kuma idan aka ce musu : " Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa , " sukan ce : " Mũ mãsu kyautatawa kawai ne ! "

(src)="s2.12"> Yet they are surely mischief-mongers , even though they do not know .
(trg)="s2.12"> To , lalle ne su , sũne mãsu ɓarna , kuma amma bã su sansancewa .

(src)="s2.13.0"> When asked to believe as others do , they say : " Should we believe like fools ? "
(trg)="s2.13.0"> Kuma idan aka ce musu : " ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni , " sukan ce : " Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni ? "

(src)="s2.13.1"> And yet they are the fools , even though they do not know .
(trg)="s2.13.1"> To , lalle ne su , sũ ne wãwãye , kuma amma bã su sani .

(src)="s2.14"> When they meet the faithful they say : " We believe ; " but when alone with the devils ( their fellows ) , they say : " We are really with you ; we were joking . "
(trg)="s2.14.0"> Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni , sukan ce : " Mun yi ĩmãni .
(trg)="s2.14.1"> " Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu , sukan ce : " Lalle ne muna tãre da ku : Mu mãsu izgili , kawai ne . "

(src)="s2.15"> But God will turn the joke against them and allow them to sink deeper into evil and wander perplexed in their wickedness .
(trg)="s2.15"> Allah Yana yin izgili gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu , suna ɗimuwa .

(src)="s2.16"> They are indeed those who bartered away good guidance for error and gained nothing from the deal , nor found the right way .
(trg)="s2.16"> Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya , sai fataucinsu bai yi rĩba ba , kuma ba su kasance masu shiryuwa ba .

(src)="s2.17"> They are like a man who kindles a fire , and when its glow has illumined the air God takes away their light leaving them in the dark where they will not be able to see .
(trg)="s2.17"> Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta , to , a lõkacin da ta haskake abin da yake gẽfensa ( na abin tsõro ) , Allah Ya tafi da haskensu , kuma Ya bar su a cikin duffai , bã su gani .

(src)="s2.18"> They are deaf , dumb and blind , and shall never return ;
(trg)="s2.18"> Kurãme , bẽbãye , makãfi , sabõda haka bã su kõmõwa .

(src)="s2.19.0"> Or like rain pouring from the sky which hides within it darkness , thunder and lightning .
(src)="s2.19.1"> They thrust their fingers into their ears for safety against noise and death .
(trg)="s2.19.0"> Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama , a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya : suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin , dõmin tsõron mutuwa .

(src)="s2.19.2"> But God surrounds those who believe not from all sides .
(trg)="s2.19.1"> Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai !

(src)="s2.20.0"> Verily the lightning could snatch away their eyes .
(src)="s2.20.1"> When it flashes forth they walk in its flare .
(trg)="s2.20.0"> Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu , ko da yaushe ta haskakã musu , sai su yi tafiya a cikinta , kuma idan ta yi duhu a kansu , sai su yi tsaye .

(src)="s2.20.2"> When darkness returns they stand still .
(trg)="s2.20.1"> Kuma dã Allah Yã so , sai Ya tafi da jinsu da gannansu .

(src)="s2.20.3"> And if the Lord wills so He could take away their hearing and sight ; surely God is all-powerful .
(trg)="s2.20.2"> Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne .

(src)="s2.21"> So , O you people , adore your Lord who created you , as He did those before you , that you could take heed for yourselves and fear Him
(trg)="s2.21.0"> Yã ku mutãne !
(trg)="s2.21.1"> Ku bauta wa Ubangjinku , Wanda Ya halicce ku , kũ da waɗanda suke daga gabãninku , tsammãninku ku kãre kanku !

(src)="s2.22.0"> Who made the earth a bed for you , the sky a canopy , and sends forth rain from the skies that fruits may grow -- your food and sustenance .
(trg)="s2.22.0"> Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa , kuma sama gini , kuma Ya saukar da ruwa daga sama , sa 'an nan Ya fitar da abinci daga ' ya 'yan itãce game da shi , sabõda ku .

(src)="s2.22.1"> So , do not make another the equal of God knowingly .
(trg)="s2.22.1"> Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi , alhãli kuwa kuna sane .

(src)="s2.23"> If you are in doubt of what We have revealed to Our votary , then bring a Surah like this , and call any witness , apart from God , you like , if you are truthful .
(trg)="s2.23.0"> Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bãwanmu , to , ku zõ da sũra guda daga misalinsa ( Alƙur 'ãni ) .
(trg)="s2.23.1"> Kuma ku kirãwo shaidunku baicin Allah , idan kun kasance mãsu gaskiya .

(src)="s2.24"> But if you cannot , as indeed you cannot , then guard yourselves against the Fire whose fuel is men and rocks , which has been prepared for the infidels .
(trg)="s2.24"> To , idan ba ku aikata ( kãwo sura ) ba , to , bã zã ku aikataba , sabõda haka , ku ji tsoron wuta , wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne , an yi tattalinta dõmin kãfurai .

(src)="s2.25.0"> Announce to those who believe and have done good deeds , glad tidings of gardens under which rivers flow , and where , when they eat the fruits that grow , they will say : " Indeed they are the same as we were given before , " so like in semblance the food would be .
(src)="s2.25.1"> And they shall have fair spouses there , and live there abidingly .
(trg)="s2.25.0"> Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai , cẽwa lallene , suna da gidãjen Aljanna , ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu .
(trg)="s2.25.1"> Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu ' ya 'yan itãce daga gare su , sai su ce : " Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka , " Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna , Kuma sunã da , a cikin su , mãtan aure mãsu tsarki , kuma su , cikin su madawwama ne .

(src)="s2.26.0"> God is not loath to advance the similitude of a gnat or a being more contemptible ; and those who believe know whatever is from the Lord is true .
(trg)="s2.26.0"> Lalle ne , Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli , kõwane iri ne , sauro da abin da yake bisa gare shi .

(src)="s2.26.1"> But those who disbelieve say : " What does God mean by this parable ? "
(src)="s2.26.2"> He causes some to err this way , and some He guides ; yet He turns away none but those who transgress ,
(trg)="s2.26.1"> To , amma waɗanda suka yi ĩmãni , sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su , kuma amma waɗanda suka kãfirta , sai su ce : " Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan ya zama misãli ? " na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi , kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi , kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai .

(src)="s2.27"> Who , having sealed it , break God 's covenant , dividing what He ordained cohered ; and those who spread discord in the land will suffer assuredly .
(trg)="s2.27"> Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi , kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sãdar , kuma suna ɓarna a cikin ƙasa , waɗannan sũ ne mãsu hasãra .

(src)="s2.28.0"> Then how can you disbelieve in God ?
(src)="s2.28.1"> He gave you life when you were dead .
(src)="s2.28.2"> He will make you die again then bring you back to life : To Him then you will return .
(trg)="s2.28"> Yaya kuke kãfirta da Allah , alhãli kuwa kun kasance matattu sa 'an nan Ya rãyar da ku , sa 'nnan kuma Ya matar da ku , sa 'an nan kuma Ya rãya ku , sa 'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku ?

(src)="s2.29"> He made for you all that lies within the earth , then turning to the firmament He proportioned several skies : He has knowledge of everything .
(trg)="s2.29.0"> Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya , sa 'an nan kuma Ya daidaita zuwa sama , sa 'an nan Y a aikata su sammai bakwai .
(trg)="s2.29.1"> Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne .

(src)="s2.30.0"> Remember , when your Lord said to the angels : " I have to place a trustee on the earth , " they said : " Will You place one there who would create disorder and shed blood , while we intone Your litanies and sanctify Your name ? "
(src)="s2.30.1"> And God said : " I know what you do not know . "
(trg)="s2.30"> Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã 'iku : " Lalle ne , Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa , " suka ce : " Ashe , zã Ka sanya a cikinta , wanda zai yi ɓarna a cikinta , kuma mu , muna yi maka tasbihi tare da gõde maka , kuma muna tsarkakewa gareka " Ya ce : " Lalle ne , Ni Na san abin da ba ku sani ba . "

(src)="s2.31"> Then He gave Adam knowledge of the nature and reality of all things and everything , and set them before the angels and said : " Tell Me the names of these if you are truthful . "
(trg)="s2.31"> Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu , sa 'an nan kuma ya gitta su a kan malã 'iku , sa 'n nan Ya ce : " Ku gaya mini sũnayen waɗannan , idan kun nasance mãsu gaskiya . "

(src)="s2.32"> And they said : " Glory to You ( O Lord ) , knowledge we have none except what You have given us , for You are all-knowing and all-wise . "
(trg)="s2.32.0"> Suka ce : " Tsarki ya tabbata a gare Ka !
(trg)="s2.32.1"> Bãbu sani a gare mu , lalle ne Kai , Kai ne Masani , Mai hikima . "

(src)="s2.33.0"> Then He said to Adam : " Convey to them their names . "
(trg)="s2.33.0"> Ya ce : " Yã Ãdam !
(trg)="s2.33.1"> Ka gaya musu sũnãyensu . "

(src)="s2.33.1"> And when he had told them , God said : " Did I not tell you that I know the unknown of the heavens and the earth , and I know what you disclose and know what you hide ? "
(trg)="s2.33.2"> To , a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu , ( Allah ) Ya ce : " Ashe , ban ce muku ba , lalle Ni , Inã sane da gaibin sammai da ƙasa , kuma ( Inã sane da ) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa ? "

(src)="s2.34"> Remember , when We asked the angels to bow in homage to Adam , they all bowed but Iblis , who disdained and turned insolent , and so became a disbeliever .
(trg)="s2.34"> Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã 'iku : " Ku yi sujada ga Ãdam , " Sai suka yi sujada , fãce Ibilĩsa ya ƙi , kuma ya yi girman kai , kuma ya kasance daga kãfirai .

(src)="s2.35"> And We said to Adam : " Both you and your spouse live in the Garden , eat freely to your fill wherever you like , but approach not this tree or you will become transgressors .
(trg)="s2.35.0"> Kuma muka ce : " Ya Ãdam !
(trg)="s2.35.1"> Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna , kuma ku ci daga gare ta , bisa wadãta , inda kuke so , kuma kada ku kusanci wannan itãciyar , har ku kasance daga azzãlumai . "

(src)="s2.36.0"> But Satan tempted them and had them banished from the ( happy ) state they were in .
(trg)="s2.36.0"> Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta , sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa .

(src)="s2.36.1"> And We said : " Go , one the antagonist of the other , and live on the earth for a time ordained , and fend for yourselves . "
(trg)="s2.36.1"> Kuma muka ce : " Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe , kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci . "

(src)="s2.37"> Then his Lord sent commands to Adam and turned towards him : Indeed He is compassionate and kind .
(trg)="s2.37.0"> Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa , sabõda haka ya karɓi tũba a kansa .
(trg)="s2.37.1"> Lalle ne Shi , Shĩ ne Mai karɓar tũba , Mai jin ƙai .

(src)="s2.38.0"> And We said to them : " Go , all of you .
(trg)="s2.38.0"> Muka ce : " Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya .

(src)="s2.38.1"> When I send guidance , whoever follows it will neither have fear nor regret ;
(trg)="s2.38.1"> To , imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni , to , wanda ya bi shiriya ta to , bãbu tsõro a kansu , kuma bã su yin baƙin ciki . "

(src)="s2.39"> But those who deny and reject Our signs will belong to Hell , and there abide unchanged . "
(trg)="s2.39"> " Kuma waɗanda suka kãfirta , kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu , waɗannan sũ ne abõkan Wuta ; sũ a cikinta madawwama ne . "

(src)="s2.40.0"> O children of Israel , remember the favours I bestowed on you .
(src)="s2.40.1"> So keep your pledge to Me , and I will mine to you , and be fearful of Me ,
(trg)="s2.40.0"> Yã Banĩ Isrã 'Ĩla !
(trg)="s2.40.1"> Ku tuna ni 'imãTa a kanku , kuma ku cika alƙawariNa , In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni , ku ji tsõro Na .

(src)="s2.41"> And believe in what I have sent down which verifies what is already with you ; and do not be the first to deny it , nor part with it for little gain ; and beware of Me .
(trg)="s2.41.0"> Kuma , ku yi ĩmãni da abin da na saukar , mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku , kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi , Kuma kada ku sayi ' yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa .
(trg)="s2.41.1"> Kuma ku ji tsõrõNa , Nĩ kaɗai .

(src)="s2.42"> Do not confuse truth with falsehood , nor conceal the truth knowingly .
(trg)="s2.42"> Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya , kuma ku ɓõye gaskiya , alhãli kuwa kuna sane .

(src)="s2.43"> Be firm in devotion ; give zakat ( the due share of your wealth for the welfare of others ) , and bow with those who bow ( before God ) .
(trg)="s2.43"> Kuma ku tsayar da salla ; kuma ku bãyar da zakka ; kuma ku yi rukũ 'i tãre da mãsu yin rukũ 'i .

(src)="s2.44.0"> Will you enjoin good deeds on the others and forget your own selves ?
(trg)="s2.44.0"> Shin , kuna umurnin mutãne da alhẽri , kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi ?

(src)="s2.44.1"> You also read the Scriptures , why do you then not understand ?
(trg)="s2.44.1"> Shin , bãzã ku hankalta ba ?

(src)="s2.45"> Find strength in fortitude and prayer , which is heavy and exacting but for those who are humble and meek ,
(trg)="s2.45.0"> Kuma ku nẽmi taimako da yin haƙuri , da salla .
(trg)="s2.45.1"> Kuma lalle ne ita , haƙĩƙa , mai girma ce fãce fa a kan mãsu tsõron Allah .

(src)="s2.46"> Who are conscious that they have to meet their Lord , and to Him they have to return .
(trg)="s2.46"> Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle ne su mãsu haɗuwa da Ubangijinsu , kuma lalle ne sũ a gareshi mãsu kõmãwa ne .

(src)="s2.47"> Remember , O children of Israel , the favours I bestowed on you , and made you exalted among the nations of the world .
(trg)="s2.47.0"> Yã banĩ Isrã 'ĩla !
(trg)="s2.47.1"> Ku tuna ni 'imaTa , wadda Na ni 'imta a kanku , kuma lalle ne Ni , na fĩfĩta ku a kan tãlikai .

(src)="s2.48"> Take heed of the day when no man will be useful to man in the least , when no intercession matter nor ransom avail , nor help reach them .
(trg)="s2.48"> Kuma ku ji tsron wani yini , ( a cikinsa ) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme , kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi , kuma ba a karɓar fansa daga gare shi , kuma bã su zama ana taimakon su ba .

(src)="s2.49"> Remember , We saved you from the Pharaoh 's people who wronged and oppressed you and slew your sons but spared your women : In this was a great favour from your Lord .
(trg)="s2.49.0"> Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir 'auna , su na taya muku muguntar azãba , su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku .
(trg)="s2.49.1"> Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku .

(src)="s2.50"> Remember , We parted the sea and saved you , and drowned the men of Pharaoh before your very eyes .
(trg)="s2.50"> Kuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku , sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir 'auna , alhãli kuwa kũ kuna kallo .

(src)="s2.51"> Yet , remember , as We communed with Moses for forty nights you took the calf in his absence ( and worshipped it ) , and you did wrong .
(trg)="s2.51"> Kuma a lõkacin da muka yi wa 'adi ga Mũsa , dare arba 'in , sa 'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa , alhãli kũ , kuna mãsu zãlunci ( da bauta masa ) .

(src)="s2.52"> Even so , We pardoned you that you may be grateful .
(trg)="s2.52"> Sa 'an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan , tsammãninku , kuna gõdẽwa .

(src)="s2.53"> Remember , We gave Moses the Book and Discernment of falsehood and truth , that you may be guided .
(trg)="s2.53"> Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabẽwa , tsammãninku , kuna shiryuwa .

(src)="s2.54.0"> Remember , Moses said : " My people , by taking this calf you have done yourselves harm , so now turn to your Creator in repentance , and kill your pride , which is better with your Lord . "
(trg)="s2.54.0"> Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa : " Ya mutãnena !
(trg)="s2.54.1"> Lalle ne ku , kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin , sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku , sai ku kashe kãwunanku .

(src)="s2.54.1"> And ( the Lord ) softened towards you , for He is all-forgiving and merciful .
(trg)="s2.54.2"> Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku .
(trg)="s2.54.3"> Sa 'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi , Shi ne Mai karɓar tũba , Mai jin ƙai .

(src)="s2.55"> Remember , when you said to Moses : " We shall not believe in you until we see God face to face , " lightning struck you as you looked .
(trg)="s2.55.0"> Kuma a lõkacin da kuka ce : " Ya Musa !
(trg)="s2.55.1"> Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka , sai munga Allah bayyane , " sabada haka tsãwar nan ta kamaku , alhãli kuwa kuna kallo .

(src)="s2.56"> Even then We revived you after you had become senseless that you might give thanks ;
(trg)="s2.56"> Sa 'an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku , tsammãninku , kuna gõdẽwa .

(src)="s2.57.0"> And made the cloud spread shade over you , and sent for you manna and quails that you may eat of the good things We have made for you .
(src)="s2.57.1"> No harm was done to Us , they only harmed themselves .
(trg)="s2.57"> Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku , kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku ; " Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku . " kuma ba su zãlunce Mu ba , kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta .

(src)="s2.58.0"> And remember , We said to you : " Enter this city , eat wherever you like , as much as you please , but pass through the gates in humility and say : ' May our sins be forgiven . '
(src)="s2.58.1"> We shall forgive your trespasses and give those who do good abundance .
(trg)="s2.58.0"> Kuma a lokacin da Muka ce : " Ku shiga wannan alƙarya .
(trg)="s2.58.1"> San nan ku ci daga gareta , idan kuka so , bisa wadata , kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu 'i , kuma ku ce ; " kãyar da zunubai " Mu gãfarta muku laifukanku , kuma zã mu ƙãra wa mãsu kyautatawa . "

(src)="s2.59"> But the wicked changed and perverted the word We had spoken to a word distorted , and We sent from heaven retribution on the wicked , for they disobeyed .
(trg)="s2.59"> Sai waɗanda suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu , saboda haka muka saukar a kan waɗanda suka yi zãlunci da azãba daga sama sabõda abin da suka kasance suna yi na fãsiƙanci .

(src)="s2.60.0"> And remember , when Moses asked for water for his people , We told him to strike the rock with his staff , and behold , twelve springs of gushing water gushed forth so that each of the tribes came to know its place of drinking .
(trg)="s2.60.0"> Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa , Muka ce ; " Ka dõki dũtsen da sandarka . "
(trg)="s2.60.1"> Sai marmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓugo , haƙĩƙa , kõwaɗanne mutãne sun san wurin shansu .

(src)="s2.60.1"> Eat and drink , ( enjoy ) God 's gifts , and spread no discord in the land .
(trg)="s2.60.2"> " Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku , kuma kada ku yi fasadi , a cikin ƙasa , kuna mãsu ɓarna . "

(src)="s2.61.0"> Remember , when you said : " O Moses , we are tired of eating the same food ( day after day ) , ask your Lord to give us fruits of the earth , herbs and cucumbers , grains and lentils and onions ; " he said : " Would you rather exchange what is good with what is bad ?
(trg)="s2.61.2"> Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta , dumanta , da alkamarta da albasarta .
(trg)="s2.61.3"> Ya ce : " Kuna nẽman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhẽri ?

(src)="s2.61.1"> Go then to the city , you shall have what you ask . "
(trg)="s2.61.4"> Ku sauka wani birni ( daga cikin birane ) , lalle ne , kuna da abin da kuka rõƙa .
(trg)="s2.61.5"> " Kuma Muka dõka musu walãƙanci da talauci .

(src)="s2.61.2"> So they were disgraced and became indigent , earning the anger of God , for they disbelieved the word of God , and slayed the prophets unjustly , for they transgressed and rebelled .
(trg)="s2.61.7"> Wancan sabõda lalle su , sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah , kuma suna kashe Aannabãwa , bãda hakki ba .
(trg)="s2.61.8"> Wancan , sabõda sãɓawarsu ne , kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi .

(src)="s2.62"> Surely the believers and the Jews , Nazareans and the Sabians , whoever believes in God and the Last Day , and whosoever does right , shall have his reward with his Lord and will neither have fear nor regret .
(trg)="s2.62"> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni , da waɗanda suka tũba , da Nasãra da Makarkata , wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira , kuma ya aikata aikin ƙwarai , to , suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu , kuma bãbu tsõro a kansu , kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba .

(src)="s2.63"> Remember the day We made the covenant with you and exalted you on the Mount and said : " Hold fast to what We have given you , and remember what is therein that you may take heed . "
(trg)="s2.63.0"> Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku , kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku : " Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi .
(trg)="s2.63.1"> Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa , tsammãninku ku kãrekanku .

(src)="s2.64"> But you went back ( on your word ) , and but for the mercy and grace of God you were lost .
(trg)="s2.64"> Sa 'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan , to , bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku , haƙĩƙa , dã kun kasance daga mãsu hasãra . "

(src)="s2.65"> You know and have known already those among you who had broken the sanctity of the Sabbath , and to whom We had said : " Become ( like ) apes despised , "
(trg)="s2.65"> Kuma lalle ne , haƙĩƙa , kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar , sai muka ce musu : " ku kasance birai ƙasƙantattu . "

(src)="s2.66"> And whom We made an example for the people ( of the day ) and those after them , and warning for those who fear God .
(trg)="s2.66"> Muka sanya ta ( mas 'alar ) azãba , dõmin abin da yake gaba gareta , da yake a bãyanta , kuma wa 'azi ga mãsu taƙawa .

(src)="s2.67.0"> Remember , when Moses said to his people : " God demands that you sacrifice a cow , " they said : " Are you making fun of us ? "
(trg)="s2.67.0"> Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa : " Lalle ne , Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya . "
(trg)="s2.67.1"> Suka ce : " Shin kana riƙon mu ne da izgili ? "

(src)="s2.67.1"> And he said : " God forbid that I be of the ignorant . "
(trg)="s2.67.2"> Ya ce : " Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai . "

(src)="s2.68.0"> " Call on your Lord for us , " they said , " that He might inform us what kind she should be . "
(trg)="s2.68.0"> Suka ce : " Ka rõƙa mana Ubangijinka , Ya bayyana mana , mecẽ ce ita ? "

(src)="s2.68.1"> " Neither old nor young , says God , but of age in between , " answered Moses .
(src)="s2.68.2"> " So do as you are bid . "
(trg)="s2.68.1"> Ya ce : " Lalle ne , Shi , Yana cewa : " Lalle ne ita sãniya ce ; bã tsõfuwa ba , bã kuma budurwa ba , tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan , ' sai ku aikata abin da ake umurninku . "

(src)="s2.69.0"> " Call on your Lord , " they said , " to tell us the colour of the cow . "
(trg)="s2.69.0"> Suka ce : " Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta . "

(src)="s2.69.1"> " God says , " answered Moses , " a fawn coloured cow , rich yellow , well pleasing to the eye . "
(trg)="s2.69.1"> Ya ce : " Lalle ne , Shi Yana cewa : " Ita wata saniya ce fatsa-fatsa , mai tsan-tsan launi , tana faranta ran mausu kallonta . "

(src)="s2.70.0"> " Call on your Lord , " they said , " to name its variety , as cows be all alike to us .
(src)="s2.70.1"> If God wills we shall be guided aright . "
(trg)="s2.70"> Suka ce : " Ka rõƙa mana Ubangijinka , Ya bayyana mana abin da yake ita , lalle ne shãnu suna yi mana kamã da jũna , kuma mu , idan Allah Yã so , haƙĩƙa , shiryuwa ne . "

(src)="s2.71.0"> And Moses said : " He says it 's a cow unyoked , nor worn out by ploughing or watering the fields , one in good shape with no mark or blemish . "
(trg)="s2.71.0"> Ya ce : " Lalle ne Shi , Yana cẽwa : " Ita wata sãniya ce ; ba horarra bã tana noman ƙasa , kuma ba ta shayar da shuka , lãfiyayya ce : bãbu wani sõfane a cikinta . "

(src)="s2.71.1"> " Now have you brought us the truth , " they said ; and then , after wavering , they sacrificed the cow .
(trg)="s2.71.1"> Suka ce : " Yanzu kã zo da gaskiya .
(trg)="s2.71.2"> Sai suka yanka ta , kamar ba zã su aikata ba .

(src)="s2.72"> Remember when you killed a man and blamed each other for the deed , God brought to light what you concealed .
(trg)="s2.72"> Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai , kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa , kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne .