# ha/ted2020-381.xml.gz
# it/ted2020-381.xml.gz


(src)="1"> Da na isa ƙasar Zimbabwe , na kasa gane yadda mutane talatin da biyar cikin ɗari na ƙasar ke da cutar ƙanjamau .
(trg)="1"> Quando sono arrivata per la prima volta nel meraviglioso Zimbabwe , mi era difficile comprendere che il 35 % della popolazione fosse sieropositiva .

(src)="2"> Sai da na samu na shiga gidajen mutane tukunna na gane yawan mutanen da ke da cutar .
(trg)="2"> Fu solo quando fui invitata nelle case della gente che iniziai a capire il costo umano dell' epidemia .

(src)="3"> Misali , wannan Herbert ne da kakarsa .
(trg)="3"> Per esempio , questo é Herbert con sua nonna .

(src)="4"> Farkon haɗuwa na da shi , yana zaune ne a kan cinyar kakarsa .
(trg)="4"> Quando lo incontrai per la prima volta , era seduto nel grembo di sua nonna .

(src)="5"> Cutar ƙanjamau ta kashe iyayensa , kakarsa ce take kula da shi kafin shi ma ya rasu ta hannun cutar .
(trg)="5"> Era rimasto orfano , perché entrambi i suoi genitori erano morti di AIDS , e così sua nonna si prese cura di lui finché anche lui morì di AIDS .

(src)="6"> Ya so zama a kan cinyarta domin wai kwanciya a kan gadonsa na yi masa zafi sosai .
(trg)="6"> Preferiva sedere nel suo grembo perchè a letto le sofferenze peggioravano .

(src)="7"> Da ta tashi domin ta dafa shayi , ta ajiye shi a kan cinyata ban taɓa ganin yaro maras nauyi kamarsa ba .
(trg)="7.1"> Quando la nonna si alzò per fare il thè , me lo mise in grembo .
(trg)="7.2"> Non avevo mai toccato un bambino tanto emaciato .

(src)="8"> Kafin in tafi , na tambaye sa idan akwai wani abin da yake so in sayo masa .
(trg)="8"> Prima di andarmene , gli chiesi se potevo portargli qualcosa

(src)="9"> Na ɗauka zai tambayi ni ma abubuwan wasa , ko kuma alewa , amma sai ya tambaye ni in kawo masa silifa , domin kafafunsa na masa sanyi .
(trg)="9"> Pensavo mi chiedesse un giocattolo , o una caramella , invece mi chiese delle pantoffole perchè aveva freddo ai piedi .

(src)="10"> Wanna Joyce ce - a cikin hoton nan - shekarun ta ashirin da ɗaya .
(trg)="10.1"> Lei é Joyce .
(trg)="10.2"> Ha 21 anni , in questa foto .

(src)="11"> Ba ta da miji , kuma tana da cutar ƙanjamau .
(trg)="11"> Era una madre single , e sieropositiva .

(src)="12"> Na ɗauki hoton ta kafin ta haifu , da kuma bayan ta haifi kyakkyawar ' yarta , Issa
(trg)="12"> L' ho fotografata prima e dopo la nascita di Issa , la sua bellissima bambina .

(src)="13"> Sati da ya wuce ina tafiya a kan titin Lafayette da ke cikin Manhattan sai wata matan da ban sani ba ta bugo min waya cewa Joyce ta rasu bayan ta cika shekaru ashirin da uku
(trg)="13"> La scorsa settimana stavo camminando per Lafayette Street , a Manhattan , e una donna , che non conoscevo , mi chiamò per dirmi che Joyce era morta a soli 23 anni .

(src)="14"> Yanzu , uwar Joyce ce ke kula da ' yarta , kamar yaran Zimbabwe da yawa waɗanda cutar ta ɗauke iyayensu .
(trg)="14"> Ora é la mamma di Joyce a prendersi cura della nipote , come capita a molti altri bambini dello Zimbabwe rimasti orfani per l' epidemia .

(src)="15"> Kaɗan kenan daga cikin labarai irin wannan .
(trg)="15"> Ecco un pò di storie .

(src)="16"> A cikin kowane hoto , akwai mutane da ke nan raye kuma suna da labarai da ya kamata a faɗa .
(trg)="16"> Dietro ogni immagine ci sono individui con vite complesse storie che meritano di essere raccontate .

(src)="17"> Duk hotunan nan daga Zimbabwe ne .
(trg)="17"> Tutte queste immagini vengono dallo Zimbabwe .

(src)="18"> Chris Anderson : Kristen , za ki iya ɗaukan minti ɗaya , ki faɗa mana yadda kika isa Afirka ?
(trg)="18"> Chris Anderson : Kirsten , vuoi raccontarci in un minuto cosa ti ha spinto in Africa ?

(src)="19"> Kristen Ashburn : Mmm , kai .
(trg)="19"> KA : Mmhh , mio Dio ...

(src)="20"> CA : kawai ki -- KA : A lokacin ina aiki ne , ɗaukan hotuna akan abubuwan da ke yayi .
(trg)="20.1"> CA : Solo ...
(trg)="20.2"> KA : In quel periodo , lavoravo per un fotografo di moda

(src)="21"> Kuma kullum nakan karanta New York Times , yawan mutanen da ke da cutar na ba ni mamaki .
(trg)="21"> Leggevo continuamente il New York Times , ed ero impressionata dalle statistiche , dai numeri .

(src)="22"> Har ya kan ba da tsoro .
(trg)="22"> Erano semplicemente sconvolgenti .

(src)="23"> Sai na bar aikina domin na gane cewa ina son yin aiki a kan cutar ƙanjamau .
(trg)="23"> Così lasciai il mio lavoro e decisi di occuparmene .

(src)="24"> Na fara zuwa Botswana inda na yi wata ɗaya -- wannan a cikin shekara 2000 ne -- kafin nan na je Zimbabwe inda na yi wata ɗaya da rabi , sannan na ƙara komawa cikin wannan wata na Maris 2002 kuma na ƙara yin wata ɗaya da rabi .
(trg)="24"> All' inizio andai in Botswana , dove restai per un mese , era nel Dicembre 2000 poi andai nello Zimbabwe per un mese e mezzo , e poi ci ritornai nel Marzo del 2002 per un altro mese e mezzo .

(src)="25"> CA : Wannan labarin na ki mai ban mamaki ne , mun gode .
(trg)="25"> CA : E' una storia incredibile , grazie .

(src)="26"> KB ; Ni ma na gode da ku ka ba ni daman zuwa wannan shirin --
(trg)="26"> KA : Grazie di avermela fatta mostrare .