# en/ted2020-381.xml.gz
# ha/ted2020-381.xml.gz


(src)="1"> When I first arrived in beautiful Zimbabwe , it was difficult to understand that 35 percent of the population is HIV positive .
(trg)="1"> Da na isa ƙasar Zimbabwe , na kasa gane yadda mutane talatin da biyar cikin ɗari na ƙasar ke da cutar ƙanjamau .

(src)="2"> It really wasn 't until I was invited to the homes of people that I started to understand the human toll of the epidemic .
(trg)="2"> Sai da na samu na shiga gidajen mutane tukunna na gane yawan mutanen da ke da cutar .

(src)="3"> For instance , this is Herbert with his grandmother .
(trg)="3"> Misali , wannan Herbert ne da kakarsa .

(src)="4"> When I first met him , he was sitting on his grandmother 's lap .
(trg)="4"> Farkon haɗuwa na da shi , yana zaune ne a kan cinyar kakarsa .

(src)="5"> He has been orphaned , as both of his parents died of AIDS , and his grandmother took care of him until he too died of AIDS .
(trg)="5"> Cutar ƙanjamau ta kashe iyayensa , kakarsa ce take kula da shi kafin shi ma ya rasu ta hannun cutar .

(src)="6"> He liked to sit on her lap because he said that it was painful for him to lie in his own bed .
(trg)="6"> Ya so zama a kan cinyarta domin wai kwanciya a kan gadonsa na yi masa zafi sosai .

(src)="7"> When she got up to make tea , she placed him in my own lap and I had never felt a child that was that emaciated .
(trg)="7"> Da ta tashi domin ta dafa shayi , ta ajiye shi a kan cinyata ban taɓa ganin yaro maras nauyi kamarsa ba .

(src)="8"> Before I left , I actually asked him if I could get him something .
(trg)="8"> Kafin in tafi , na tambaye sa idan akwai wani abin da yake so in sayo masa .

(src)="9"> I thought he would ask for a toy , or candy , and he asked me for slippers , because he said that his feet were cold .
(trg)="9"> Na ɗauka zai tambayi ni ma abubuwan wasa , ko kuma alewa , amma sai ya tambaye ni in kawo masa silifa , domin kafafunsa na masa sanyi .

(src)="10"> This is Joyce who 's -- in this picture -- 21 .
(trg)="10"> Wanna Joyce ce - a cikin hoton nan - shekarun ta ashirin da ɗaya .

(src)="11"> Single mother , HIV positive .
(trg)="11"> Ba ta da miji , kuma tana da cutar ƙanjamau .

(src)="12"> I photographed her before and after the birth of her beautiful baby girl , Issa .
(trg)="12"> Na ɗauki hoton ta kafin ta haifu , da kuma bayan ta haifi kyakkyawar ' yarta , Issa

(src)="13"> And I was last week walking on Lafayette Street in Manhattan and got a call from a woman who I didn 't know , but she called to tell me that Joyce had passed away at the age of 23 .
(trg)="13"> Sati da ya wuce ina tafiya a kan titin Lafayette da ke cikin Manhattan sai wata matan da ban sani ba ta bugo min waya cewa Joyce ta rasu bayan ta cika shekaru ashirin da uku

(src)="14"> Joyce 's mother is now taking care of her daughter , like so many other Zimbabwean children who 've been orphaned by the epidemic .
(trg)="14"> Yanzu , uwar Joyce ce ke kula da ' yarta , kamar yaran Zimbabwe da yawa waɗanda cutar ta ɗauke iyayensu .

(src)="15"> So a few of the stories .
(trg)="15"> Kaɗan kenan daga cikin labarai irin wannan .

(src)="16"> With every picture , there are individuals who have full lives and stories that deserve to be told .
(trg)="16"> A cikin kowane hoto , akwai mutane da ke nan raye kuma suna da labarai da ya kamata a faɗa .

(src)="17"> All these pictures are from Zimbabwe .
(trg)="17"> Duk hotunan nan daga Zimbabwe ne .

(src)="18"> Chris Anderson : Kirsten , will you just take one minute , just to tell your own story of how you got to Africa ?
(trg)="18"> Chris Anderson : Kristen , za ki iya ɗaukan minti ɗaya , ki faɗa mana yadda kika isa Afirka ?

(src)="19"> Kirsten Ashburn : Mmm , gosh .
(trg)="19"> Kristen Ashburn : Mmm , kai .

(src)="20"> CA : Just -- KA : Actually , I was working at the time , doing production for a fashion photographer .
(trg)="20"> CA : kawai ki -- KA : A lokacin ina aiki ne , ɗaukan hotuna akan abubuwan da ke yayi .

(src)="21"> And I was constantly reading the New York Times , and stunned by the statistics , the numbers .
(trg)="21"> Kuma kullum nakan karanta New York Times , yawan mutanen da ke da cutar na ba ni mamaki .

(src)="22"> It was just frightening .
(trg)="22"> Har ya kan ba da tsoro .

(src)="23"> So I quit my job and decided that that 's the subject that I wanted to tackle .
(trg)="23"> Sai na bar aikina domin na gane cewa ina son yin aiki a kan cutar ƙanjamau .

(src)="24"> And I first actually went to Botswana , where I spent a month -- this is in December 2000 -- then went to Zimbabwe for a month and a half , and then went back again this March 2002 for another month and a half in Zimbabwe .
(trg)="24"> Na fara zuwa Botswana inda na yi wata ɗaya -- wannan a cikin shekara 2000 ne -- kafin nan na je Zimbabwe inda na yi wata ɗaya da rabi , sannan na ƙara komawa cikin wannan wata na Maris 2002 kuma na ƙara yin wata ɗaya da rabi .

(src)="25"> CA : That 's an amazing story , thank you .
(trg)="25"> CA : Wannan labarin na ki mai ban mamaki ne , mun gode .

(src)="26"> KB : Thanks for letting me show these .
(trg)="26"> KB ; Ni ma na gode da ku ka ba ni daman zuwa wannan shirin --